✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Bankin Switzerland ya tafka asara mafi muni a shekara 115

Sama da shekara 115 ke nan rabon da ya tafka irin wannan asarar

Babban Bankin kasar Switzerland ya ce ya tafka asarar biliyan 132 a kudin kasar, kawatankwacin Dalar Amurka biliyan 143 a shekarar 2022.

Bankin ya bayyana haka ne ranar Litinin, inda ya ce rabonsa da ganin irin haka tun shekara 115 da suka gabata.

A cewar bankin, koma bayan da aka fuskanta a  kasuwar hada-hadar kudi na daga cikin dalilan da suka haddasa masa wannan babbar asarar.

Alkaluman da bankin ya fitar ranar Litinin, sun nuna asar da bankin ya yi na kudin kasar biliyan 26 a 2021, ta fi ta 2015 inda ya rasa biliyan 23 a kudin kasar.

Sakamakon asarar da ya tafka na nufin babban bankin ba zai biya gwamnatocin kasar da na yanki-yanki kudaden da ya saba ba su ba, in ji masu fashin baki.

Kasuwannin hannayen jari na duniya sun yi rauni, kuma farashin lamuni ya fadi a bara, yayin da manyan bankunan duniya suka kara yawan kudin ruwa don yaki da hauhawar farashin kayayyaki.