Babban dan Farfesa Ango Abdullahi ya rasu | Aminiya

Babban dan Farfesa Ango Abdullahi ya rasu

Isah Ango Abdullahi
Isah Ango Abdullahi
    Aliyu Babankarfi, Zariya

Isah, babban dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya rasu.

Isah Ango Abdullahi ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Abuja ranar Alhamis da dare.

Wani makusancin iyalan ya ce a safiyar Juma’a za a kai gawar mamacin mahaifarsa, Zariya, inda za a yi masa Sallah.

Ana sa ran gudanar da Sallar Jana’izarsa bayan kammala Sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Haruna Danja da ke Tudun Wada, Zariya.

Kafin rasuwarsa, marigayin Isah Ango Abdullahi ma’aikaci ne a Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Kasa (NIA).

Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya da dama.