✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban dan Farfesa Ango Abdullahi ya rasu

Isah, babban dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya

Isah, babban dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya rasu.

Isah Ango Abdullahi ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Abuja ranar Alhamis da dare.

Wani makusancin iyalan ya ce a safiyar Juma’a za a kai gawar mamacin mahaifarsa, Zariya, inda za a yi masa Sallah.

Ana sa ran gudanar da Sallar Jana’izarsa bayan kammala Sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Haruna Danja da ke Tudun Wada, Zariya.

Kafin rasuwarsa, marigayin Isah Ango Abdullahi ma’aikaci ne a Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Kasa (NIA).

Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya da dama.