✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babban Dan tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya rasu

Tuni dai masu fada a ji a Najeriya suka fara mika ta'aziyarsu ga Sanata David Mark.

Tunde Mark, babban da ga tsohon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, David Mark ya rasu ranar Juma’a  bayan fama da cutar sankara.

Tuni dai masu fada a ji a Najeriya suka fara mika ta’aziyarsu ga mahaifin margayin, Sanata David Mark.

Cikin wata sanarwa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP Atiku Abubakar, ya fitar, ya ce, “Na kadu da mutuwarsa, domin ni da Tunde muna da kyakykyawar alakar da ta sa na dauke shi a matsayi dan cikina.

“Addu’ata ce ga mahaifinsa shi ne Allah, ya ba shi hakurin jure rashin, shi kuma margayin, Ya ji kan sa, Ya sa mutuwar ta zamo hutu gare shi,” in Atiku, ta sanarwar da kakakinsa ya fitar a Abuja.