✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Hafsan Tsaron Indiya, matarsa da sojoji 11 sun mutu a hatsarin jirgi

Rundunar Sojin Saman kasar ce ta tabbatar da mutuwar tasu.

Rundunar Sojin Saman kasar Indiya ta tabbatar da mutuwar Babban Hafsan Tsaron kasar, Janar Bipin Rawat, matarsa da wasu manyan sojojoi 11 a wani hatsarin jirgin sama.

Hatsarin dai ya auku ne ranar Laraba a Jihar Tamil Nadu da ke kasar.

A wani gajeren sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, hatsarin ya faru ne da tsakar ranar Laraba, lokacin da jirgin ya fado a kan hanyarsa ta zuwa sansanin sojin saman kasar daga makarantar horar da jami’an sojin.

Tuni dai hukumomin kasar suka ce an kaddamar da bincike da nufin gano musabbabin hatsarin.

Firaministan Indiya, Nanendra Modi ya bayyana marigayi Rawat a matsayin hazikin soja kuma dan kishin kasa wanda ya taka rawa wajen zamanantar da rundunar sojin kasar.

Shi ma da yake tsokaci a kan hatsarin, Ministan Tsaron kasar, Rajnath Singh, ya ce, “Na kadu matuka da mutuwar Babban Hafsan Tsaron kasarmu, Janar Bipin Rawat, matarsa da wasu jami’an sojoji 11 a hatsarin jirgin sama a Jihar Tamil Nadu.”