✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban jami’in dan sanda ya fada hannun masu garkuwa a Edo

Wani babban jami’in dan sanda ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Edo da ke Kudancin Najeriya. Aminiya ta samu cewa lamarin ya…

Wani babban jami’in dan sanda ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.

Aminiya ta samu cewa lamarin ya auku ne a yayin da wasu ’yan bindiga suka fada gidan babban jami’in, ASP Clement Amoko da safiyar ranar Lahadi kuma suka yi awon gaba da shi a gaban iyalansa.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa maharan da suka yi awon gaba da jami’in sun tuntubi ’yan uwansa inda suke neman biyan fansa.

Tuni dai ’yan sanda a Jihar Edo sun dukufa wajen gudanar da ayyukan ceto abokin aikin nasu cikin gaggawa.

Jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Princewill Osaigbovo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, “Shugaban caji ofis na Ogida ya tabbatar min da faruwar lamarin kuma an fara gudanar da bincike domin ceto jami’in.”