✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban jigon Darikar Tijjaniya ya kwanta dama

Jagoran Tijjaniya Sheikh Khalifa Ahmad Tijjani bin Sheikh Ibrahim Abdullahi Inyas ya rasu

Allah Ya yi wa babban malamin addinin Musulumcin nan na kasar Senegal kuma Babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass, Sheikh Khalifa Ahmad Tijjani bin Sheikh Ibrahim Abdullahi Inyas, rasuwa.

Shaikh Khalifa Ahmad Tijjani ya rasu ne a kasar ta Senegal a daren Lahadi bayan ya yi fama da jinya.

Kafin rasuwarsa shi ne shugaban  mabiya darikar Tijjaniyya wadanda aka kiyasta sun kai kusan miliyan 100 a fadin duniya.

Khalifa Ahmad Tijjani Ibrahim Abdullahi Inyas shine jagoran darikar Tijjaniya na biyar kana wanda zai gaje shi a matsayin Khalifa na shida kani ne gare shi mai  suna  Sheikh Mahi  Ibrahim Inyas

Nan ba da jimawa ba ake sa ran iyalansa za su sanar da lokacin jana’izarsa a bisa tanade-tanaden addinin Musulunci.