✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Sakataren Izala, Mukhari Ibrahim ya rasu

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah Ya yi wa Babban Sakataren Gudanarwa na kungiyar Izala Malam Mukhari Ibrahim (Vom) rasuwa. Marigayin shi ne Babban…

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah Ya yi wa Babban Sakataren Gudanarwa na kungiyar Izala Malam Mukhari Ibrahim (Vom) rasuwa.

Marigayin shi ne Babban Sakataren Gudanarwa na Kungiyar Jama’aatu Izalatil Bid’a Wa ikamatis Sunnah (JIBWIS), tun farkon kafa kungiyar har zuwa lokacin rasuwarsa.

Mataimakin Shugaban JIBWIS, Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe, ya sanar da cewa za’a yi sallar jana’izar marigayim a masallacin Juma’ah na JIBWIS da ke Gwallaga a cikin garin Bauchi.

Sallar jana’aizar za ta gudana ne da misalin 1.00 na ranar Alhamis 11 ga watan Yunin da muke ciki.