✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Sallah: Hukumar NSCDC ta tura jami’ai 30,000 domin sintiri

Hukumar Tsaro ta Civil Defence ta girke jami'anta 30,000 don samar da tsaro a lokacin bukukuwan Babbar Sallah a Najeriya.

Hukumar Tsaro ta Civil Defence ta girke jami’anta 30,000 don samar da tsaro a lungu da sakon Najeriya a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.

Shugaban Hukumar, Ahmed Abubakar Audi, ya umarci kwamnadojin rundunar a jihohi da daraktoci masu kula da yankuna da su tabbata su tura wadatattun jami’a domin dakile duk wata barazanar tsaro a lokacin bukukuwan.

“Mun zage damtse domin tabbatar da tsaro da amincin muhimam abubuwa a lokacin bukukuwan Babbar Sallah,” in ji shi.

Audi ya ce wuraren da za a girke jami’an hukumar domin samar da tsaro sun hadda da masallatan idi da wuraren shakatawa da kasuwanni da tashoshin mota da manyan shagunan kasuwanci da sauransu.

A wurare masu rafuka kuwa, ya ba da umarnin a tura jiragen ruwa domin gudanar da sintiri da dakile ayyukan ’yan fashin teku da barayin danyen mai da dangoginsu.

Ya ce, “Karuwan hare-haren da aka samu da ke barazana ga rayuka da dukiyoyi a baya-bayan nan na bukatar daukar matakan dakile aukuwar miyagun laifuka, tun kafin a aikata su.

“Don haka ya kamata mu gano duk wasu wurare masu hadari mu dauki matakan dakile barazanar da kuma kare mutane da babu ruwansu.

“’Yan Najeriya sun cancanci samun isasshen tsaro don haka bai kamata mu bari ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda da bata-gari su cutar da su ta kowace hanya a lokacin bukukuwan.

“Na ba da umarnin a girke jami’ai 30,000 domin samar da tsaro a lungu da sakon Najeriya”, in ji Audi.