Babbar matar Sarkin Ningi ta riga mu gidan gaskiya | Aminiya

Babbar matar Sarkin Ningi ta riga mu gidan gaskiya

    Hassan Ibrahim, Bauci da Sagir Kano Saleh

Allah Ya yi wa uwar gidar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya wato Hajiya Hajiya Hama rasuwa.

Hajiya Hama, wadda Sarkin ya aura tun a shekarar 1952, ta rasu ne tana da shekara 85 a ranar Litinin.

Ta rasu ta bar ’ya’ya takwas cikinsu har da Chiroman Ningi, Alhaji Haruna Yunusa da kuma Damburam Ningi, Alhaji Yusuf Yunusa.

Sanarwar rasuwar Hajiya Hama da Masarautar Ningi ta fitar a ranar Talata ta ce an yi janai’zar ta a Fadar Sarkin Ningi a safiyar Talata kamar yadda addinin Islama ya tanadar.