✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babbar mota ta hallaka wani mutum

An yi nasarar cafke direban motar bayan ya yi yunkurin tserewa.

Wata babbar mota da ke gudun wuce ka’ida ta take wani mutum inda nan take ya ce ga garinku nan a Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.

Wani ganau ya ce motar kirar IVECO na gudun wuce kima ne lokacin da ta kwace ta take mutumin da ke kokarin tsallaka titi.

“Gudun wuce kima ne ya jawo motar ta kwace,” inji shi.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kiyaye Hadura ta FRSC na jihar, Florence Edor, ta bayyana cewa mutum uku ne hatsarin ya ritsa da su.

A cewarta, jami’an Hukumar sun cafke direban babbar motar, kuma an kai mutumin da ya take asibitin Lourdes da ke Ihiala inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Kwamandan FRSC na jihar, Andrew Kumapayi, ya jajanta wa iyalan wanda mamacin tare da jan hankalin masu tuka ababen hawa a kan gudun wuce kima.

Ya kara da cewa yin tafiya a hankali shi ne abin da ya fi dacewa a cikin gari, kuma ana samun sauki a duk lokacin da hatsari ya auku.