✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu abin daga hankali a sabon nau’in Coronavirus na Omicron —Biden

Shugaba Biden ya ce wa Amurkawa babu abin daga hankali a kan cutar.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci ’yan kasar da su kwantar da hankulansu game da yaduwar sabon nau’in cutar Coronavirus na Omicron, domin kuwa ya ce gwamnatinsa a shirye take ta dakile sabuwar barazanar.

Shugaba Biden ya ce wa Amurkawa babu abin daga hankali a kan cutar a daidai lokacin da sabon nau’inta na Omicron ke yaduwa cikin gaggawa, inda kawo yanzu ta bulla a kasashe da dama.

“Ya kamata kowanenmu ya damu da wannan cuta ta Omicron, amma kada kowa ya daga hankalinsa,” a cewar Biden cikin jawaban da ya gabatar a Fadar White House.

Ya tabbatar wa da Amurkawa cewa sabon nau’in cutar ba zai mayar da kasar baya ba kamar yadda ta kasancewa a watan Maris na 2020.

Yayin jawabin na ranar Talata, Shugaba Biden ya sanar da wasu sabbin matakan yaki da cutar ciki har da jigilar shigar da karin kayan gwaje-gwajen gaggauta gano kwayoyin cutar da adadinsu ya kai rabin biliyan wadanda za a rika amfani da su ga mutane kyauta.

Biden ya kuma ce, gwamnatinsa za ta tura jami’an soji zuwa asibitoci, da kuma jigilar kayayyaki zuwa jihohin da ke fama da hauhawar adadi na masu kamuwa da cutar domin samar da karin cibiyoyin gwajin cutar kyauta.

Shugaban ya kuma ce, Amurka za ta ba da Dala miliyan 580 a cikin karin taimako ga kungiyoyin kasa da kasa don yakar annobar, shirin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya tabbatar.

Bincike dai ya nuna cewar, fiye da kashi 73 na adadin mutanen da suka kamu da cutar Korona cikin makon da ya gabata a Amurka, sun harbu ne da sabon nau’in cutar na Omicron.