✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu barazanar da za a yi mana kan ci gaba da mulki a 2023 – Dattawan Arewa

“Muna da yawan jama’a, kuma dimokradiyya ta ta’allaka ne ga yawa.

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce babu abin da zai faru idan Arewacin Najeriya ya ci gaba da mulkin Najeriya a shekarar 2023.

Kakakin kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana hakan a karshen mako yayin da yake jawabi a taron lakca kan shugabanci na Yusuf Maitama Sule da reshen dalibai na Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ya shirya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Kiraye-kiraye dai sun fara yawa a ’yan kwanakin nan kan yankin da yakamata ya fitar da Shugaban Kasa na gaba idan Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

Yayin da Arewa ke hankoron ci gaba da mulki, su kuwa jiga-jigan siyasar Kudancin kasar nan suma sun ja layi kan tilas mulkin ya koma yankinsu.

To sai dai Dokta Hakeem ya ce ba za su amince a barsu da Mataimakin Shugaban Kasa ba a 2023 duk da cewa suna da yawan jama’ar da za su iya tsayar da dan takara kuma su lashe zaben.

Ya ce, “Arewa ba ta sayarwa ba ce kuma duk masu jiran lokacin zabe ya zo mutane su hau layi su raba musu kudi za su sha mamaki.

“Muna da yawan jama’a, kuma dimokradiyya ta ta’allaka ne ga yawa. To wanne dalili ne zai sa mu tsaya a mataki na biyu alhalin za mu iya neman matakin farko kuma mu yi nasara?

“Me zai sa wani ya yi mana barazana. Za mu nemi shugabancin kuma mu kaskantar da kai, ai Allah ne yake ba da mulkin. Mun gaje shi, amma shiru-shiru ba hauka ba ne.

“Akwai masu tunanin za su iya sayenmu saboda tattalin arzikin na cikin tsaka mai wuya, muna fama da kalubalen tsaro. Suna tafka babban kuskure.

“Ko Arewa ta ci gaba da mulki a 2023 ko a’a, duk mai son ballewa daga kasar nan dole zai ci gaba da neman dalilan yin haka. Mulki Dimokradiyya ake yi, idan ba sa jin dadin yadda lamura ke tafiya za su ci gaba da wannan tunanin. Amma ba ruwanmu da su. Mun san ai mulki Dimkoradiyya ake yi.