✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu karbi tubar ’yan bindiga ba, kashe su za mu yi —El-Rufai

Gwamnan Kaduna ya ce dan bindigar da aka kashe kawai shi ne tubabbe

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi watsi da batun karbar tubar ’yan bindiga, yana mai cewa kashe su kawai za a yi.

El-Rufai ya ce gwamnatin jiharsa ba ta yarda ba tubar ’yan ta’adda ba kuma ba ta da niyyar karbar tubar duk wani dan bindiga.

“Babu wani wanda za a so a ce mana tubabben dan ta’adda ne. A wurinmu, dan bindigar da aka kashe kawai shi ne tubabbe. Abin da muke so kawai shi ne mu kashe su, su je lahira su hadu da Allah,” inji gwamnan.

Ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban kasa inda ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari bayan harin da ’yan bindiga suka kashe mutum 40 a Karamar Hukumar Giwa ta jiharsa.

El-Rufai tare da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan jihar, Samuel Aruwan, ya ce ayyana ’yan bindiga da kotu ta yi a matsayin ’yan ta’adda ya ba wa sojoji karin karfin ragargazar su babu kakkautawa.

Saboda haka ya bukaci sojojin da kada su raga wa duk wani dan bindiga a Jihar Kaduna.

A cewarsa, sojoji na sane da inda ’yan bindigar suke boye, amma ya yi karin haske cewa jami’an tsaro suna taka-tsantsan ne domin guje wa kashe fararen hula a kokarin hallaka bata-garin.

Ya roki Gwamnatin Tarayya ta tura karin jami’an tsaro, sannan ta kara daukar sabbin ’yan sanda da sojoji saboda karancinsu ba zai ba su damar gudanar da aikinsu cikin nasarar da ake bukata ba.

‘Kalaman El-Rufai abin takaici ne’

Sai dai wani masanin harkar tsaro, Kabir Adamu, ya ce kiran da El-Rufai ya yi na kashe ’yan bindiga abin takaici ne a karkashin tsarin dimokuradiyya, wadda ke da dokoki da suka hana a kashe mai laifi ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ta kama shi da laifin ba.

A cewarsa, “Fitowar wannan magana daga mutumin da ya rantse cewa zai kare kundin tsarin mulki wanda ya riga ya tanadi yadda za a hukunta masu laifi, abin takaici ne.

“A iya sanina, kotu ce kadai ke iya ba da umarin zartar da hukuncin kisa, don haka abin takaici ne wani gwamna ya fito yana cewa wai kisa shi ne mafita.

“Idan har ana kashe mutum kafin a tsare shi a gurfanar da shi a gaban kotu, to bai kamata tsarin dimokuradiyya ya bar hakan na faruwa ba, saboda ba a so a salwantar da ran wani, sai idan har yin hakan ya zama tilas.

“Saboda haka ina shawartar zababbun shugabanni da su kauce wa duk wani abu na kisa ba tare da umarnin kotu ba.

“Idan har jami’an tsaro za su yi wani aikin soji, to ya kasance manufarsu ta farko ita ce kama mai laifi sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.

“A bari kotuna su zama su ne za su kama mutum da laifi da kuma alkalancin ko kisa ne hukuncin da ya dace da laifinsa.

 

Daga Sagir Kano Saleh da Muideen Olaniyi (Abuja); Maryam Ahmadu-Suka da Mohammaed I. Yaba (Kaduna).