✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu bukatar ja-in-ja kan tuban ’yan Boko Haram —Lawan

Shugaban Majalisar ya ce ajiye makaman Boko Haram babbar nasara ce.

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya ce babu bukatar mutane su tayar da jijiyar wuya game da karbar tubabbun ’yan Boko Haram.

Ya ce ajiye makamai da Boko Haram ke yi wata nasara ce da ya kamata a karbe ta hannu bibbiyu, domin hakan na nuni da cewa ta’addanci ya kusa zuwa karshe.

Latsa nan domin sauraron: ‘Yadda CBN ke Shirin Kaddamar Da Kudin Intanet na E-Naira’:

Ya ce, “Tubar Boko Haram wata nasara ce ga Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Borno na kawo karshen zubar da jinin da aka dade ana yi.”

Lawan ya bayyana haka ne a Maiduguri, yayin ziyarar da ya kai zuwa Fadar Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi, ranar Litinin kamar yadda hadiminsa kan kafafen watsa labarai ya sanarn.

Shugaban Majalisar ya kai ziyarar ce don yin jaje da ta’aziyya ga Shehun kan rasuwar dan uwansa Ambasada Babagana Kingibe.

A cewarsa, daga cikin tubabbun ’yan Boko Haram din da aka gano ba su da matsala za a mayar da su cikin al’umma don ci gaba da rayuwa, wadanda kuma aka gano suna da matsala za a bi hanyar da shari’a ta gindaya a kan irinsu.

“Wadanda suke da matsala sai a bi matakin shari’a a kansu, wadanda kuma ba su da matsala, da suka ajiye makamansu sai a karbi tubarsu.

“Babu bukatar yin takaddama kan me ya kamata mu yi da wadanda suka tuba.

“A kowane irin yaki ajiye makami wani salo ne na samun nasara, don haka za mu yi duk abin da ya dace don ganin an samu karin wadanda za su ajiye makamai don dawo da ci gaba a jihohin da abun ya shafa.”