✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu gudu ba ja da baya a kan ranakun zaben 2023 – Yakubu

Ya ce hatta matsalar karancin kudi da ta fetur ba za su shafi zaben ba

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce za a gudanar da babban zaben 2023 kamar yadda aka tsara.

Ya ce za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisun tarayya ranar 25 ga watan Fabrairu, sai kuma na Gwamnoni da na ’yan majalisar jiha ranar 11 ga watan Maris.

Ya bayyana hakan ne ranar laraba, lokacin da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa bayan ya kammala jawabi ga taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da Shugaban Kasa Muhammadu buhari ya jagoranta a Abuja.

Farfesa Yakubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa za a gudanar da zaben ba tare da wani tarnaki ba.

Ya kuma ba mahalarta taron tabbacin cewa wahalar man fetur da ta karancin kudin da ake fama da ita a yanzu ba za ta shafi gudanar da zaben na wata mai zuwa ba.

Da aka tambaye shi abin da suka tattauna yayin taron, Shugaban na INED ya ce, “Taro ne na jawabin halin da muke ciki kamar yadda aka saba yi idan zabe ya karato bisa al’ada. An gayyaci hukumar ne don tabyi jawabi kan shirye-shiryenta.

“An kuma gayyace mu mu yi wa Majalisar Magaban Kasa jawabi, amma su nasu zai zo ne ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairu. A takaice dai a kan shirye-shiryen zabe ne.

“Mun yi kyawawan tanade-tanade don ganin dukkan wasu matsaloli da ake da fargaba a kansu ba su zame mana tarnaki ba.

“A takaice, akwai matsaloli biyu da ke yi mana barazana. Wahalar man fetur; mun riga mun tattauna da kungiyar direbobi ta kasa, inda suka yi mana korafi a kai, kuma Alhamdulillahi mun yi magana da NNPC, sun kuma ba mu tabbacin ba za a sami matsala ba.

“Sannan game da batun karancin kudin da ake fama da shi kuwa, CBN ya yi alkawarin samar mana da tsabar duk kudaden da muke bukata yayin aikinmu na zabe,” in ji Farfesa Yakubu.

Jawabin nasa na zuwa ne yayin da ya rage kwana 17 kafin babban zaben mai zuwa.