✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu gudu ba ja da baya kan wa’adin tsofaffin kudade – Emefiele

Emefiele ya ce CBN ba zai kara wa'adin daina amfani da tsofaffin kudaden ba.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya kan wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudade a ranar 31 ga watan da muke ciki.

Emefiele ya jaddada kudurin babban bankin na daina amfani da kudade a ranar Talata a Abuja.

Ya ce “Ba ni da wani sabon labari ga wadanda suke so a tsawaita kwanakin daina karbar tsofaffin takardun kudade.

“Mutane sun tara kudade a gidajensu kuma suna sane da cewar ba su da lasisin yin hakan.”

Ya ce CBN ya samu nasarar karbar sama da tiriliyan 1.5, kuma yana sa ran cimma tiriliyan 2 kafin wa’adin ya cika a karshen watan nan.

Ya ce “Mun roki Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa (EFCC) da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) da kada su musgunawa kowa kan mika tsofaffin kudaden bankuna, kuma saboda ni sun tabbatar da min ba za su yi komai ba,” in ji shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da jama’a da dama ke korafin cewar wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin kudaden ya yi kadan, inda mutane suke tsimayin a kara wa’adin.