✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu hannun Fulani a harin da aka kai wa Gwamnan Binuwai – Miyetti-Allah

A ranar Asabar ne dai aka kai wa Gwamnan hari a kusa da gundumar Tyomu lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Gboko

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Najeriya reshen jihar Binuwai, Risku Mohammed ya musanta zargin da ake yi cewa Fulani ne suka kai wa ayarin Gwamnan jihar, Samuel Ortom hari.

A ranar Asabar ne dai aka kai wa Gwamnan hari a kusa da gundumar Tyomu lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Gboko zuwa Makurdi da tsakar rana.

Risku Mohammed a wata tattaunawa ta  wayar salula ya shaidawa wakilinmu cewa ya yi tafiya zuwa jihar Nasarawa kuma ba shi ma da masaniya a kan harin.

“Idan Gwamnan ya ce an kai masa harin ne a kan hanyarsa ta zuwa gona to ta yaya Fulani za su kai mishi harin? Ta yaya suka san inda ma za shi? Babu hannun Fulani a ciki,” inji shugaban.

A baya dai Gwamna Ortom ya sha zargin kungiyar ta Miyetti-Allah da kitsa makamantan wadannan hare-haren ko da yake sun sha musanta hakan.