✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu hannuna a kisan masu zanga-zanga —Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nesanta kansa da kisan masu zanga-zangar Lekki da jami’an tsaro suka yi a jihar Legas.…

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nesanta kansa da kisan masu zanga-zangar Lekki da jami’an tsaro suka yi a jihar Legas.

Tinubu ya bayyana haka ne a yayin tattaunawarsa ta wayar tarho da gidan talabijin na Channels a safiyar Laraba.

“Ban ga dalilin da zai sa sojoji su harbin masu zanga-zanga ba.

“Ba ni da hannu a wannan mummunan aiki, kuma ba zan taba zama daga cikin masu aikata mummunan lamari irin wannan ba”, inji Tinubu.

Ya kara da cewa “yau kusan kwana 13 zuwa 14 da fara zanga-zangar #EndSARS, wanda wasu suka yi amfani da ita wajen kai kara ta wurin Shugaban Kasa cewar ina da hannu wajen assasa zanga-zangar da ake yi”.

Ya ce hakan ne ya sa ya bawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawarar kan yadda za a magance matsalar har ta kai ga gwamnan ya kafa kwamitin bincike game da cin zarafin da ’yan sanda suka yi.

Rahotanni sun nuna kalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, wasu sama da 30 kuma sun samu rauni sakamakon bude wuta da sojoji suka yi a kan masu zanga-zanga a unguwar Lekki da misalign karfe 7 na dare a ranar Talata.

A wasu sassa na kasar nan da suka hada da Kano, Abuja, Benin, Akure, Ibadan, Jos da wasu garuruwa, bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar wajen ta da tarzoma tare da balle shagunan mutane suna satar kaya.

A wasu wuraren kuwa, bata-garin sun kona ofishin ’yan sanda tare da fasa bankuna, wanda shi ne babban dalilin da ya sa wasu jihohi sanya dokar hana fita.