✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu hannunmu a tarwatsa zanga-zangar daliban Gidan Waya – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jihar na jiran rahoton abin da ya haddasa rikici yayin zanga-zangar.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke yawo cewar ta aike da jami’an tsaro su tarwatsa zanga-zangar daliban Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya a Jihar, wacce har ta yi sanadin rasuwar wani dalibi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce gwamnatin na jiran sakamakon bincike don gano abin da ya haddasa rikici a yankin.

  1. Hatsarin mota ya lakume rayukan ’yan Najeriya 2,233 a wata 4
  2. Gwamnatin Najeriya ta kara tsananta matakan yaki da cutar Coronavirus

“Rahoton da muka samu shi ne dalibi daya ya rasu, wasu kuma sun ji rauni, yayin da jami’an tsaro uku suma suka samu rauni,” a cewarsa.

Sanarwar ta bayyana cewar Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufa’i ya mika sakon ta’aziyya ga iyayen dalibin da suka rasu, sannan ya yi wa wanda suka samu rauni fatan samun sauki.

“A yanzu haka Gwamna yana jiran rahoto daga wajen sojoji, ’yan sanda, DSS, hukumar kwalejin da kuma kungiyar daliban kwalejin.

“Gwamnati za ta fadada nata binciken bayan samun rahoto daga kowanne bangare, don daukar matakin da ya dace,” inji sanarwar.