✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu hujja a kyale talaka cuta ta kashe shi —Dokta Amina

Ta ce babu dalili hukuma ta bari cututtuka suna kashe mutane saboda su takalawa ne

A yayin da Ranar Lafiya ta Duniya ta sake zagayowa, Dokta Amina Mohammed Baloni ta ce babu dalili a rika bari cututtuka suna kashe mutane saboda su takalawa ne.

Dokta Amina Baloni wadda ita ce Kwamishinar Lafiyar ta Jihar Kaduna, ta bayyana wa Aminiya cewa babu wani uzuri da zai sa samun ingantaccen kiwon lafiya ya gagari talaka, har ta kai ga rashin lafiyar da ke damun sa ta yi ajalinsa.

Ta fadi hakna ne a yayin wata ganawa game da ranar da aka ware domin wayar da kai da kuma ganin al’umma na samun ingantacciyar kulawa a bangaren lafiya da kuma kokarin Gwamnatin Jiharta na samar da daidaito da kuma nagartaceccen bangaren kiwon lafiya.

Yaya za ki alakanta taken Ranar Lafiya ta Duniya ta bana da halin da ake ciki a Jihar Kaduna ta bangaren samar da ingantaccen kulawa da lafiya ba tare da bambanci ba?

Taken Ranar Lafiya ta Duniya ta bana shi ne ‘Samar da Karin Adalci da Lafiya a Duniya’, na nuni ga ’yancin kowane muutm na samun lafiya, da kula da lafiyarsa a wurin da yake so kuma a lokacin da yake bukata ba tare da la’akari da karfin aljihunsa ko matsayinsa ba.

A Jihar Kaduna mun yi wasu tsare-tsare da shirye-shirye a bangaren kiwon lafiya a kokarin da muke yi na tabbatar da samun daidaito a bangaren samun kula da lafiya.

Muna da cibiyoyin kula da lafiya 1,000 a fadin jihar, kowace gunduma na da akalla Cibiyar Kulda da Lafiya a Matakin Farko guda daya da aka daga darajarsa aka kuma wadata shi da kayan aiki domin saukaka samun kula da lafiya a ko’ina.

Baya ga manyan asibitoci da na kauyuka da ake da su a kowace Karamar Hukuma, Jihar na da Asibitin Koyarwa na Barau Dikko domin kula da manyan matsaloli.

Allah Ya kuma huwace wa Jihar Kaduna manyan asibitoci na taraya kamar Asibitin Ido na Kasa, Asibitn Kunne, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Asibitin Sojoji na 44, da Asibitin Sojojin Sama.

Asibitocin suna kulawa da lafiyar jama’ar Kaduna; a wuraren da ba su da su kuma ana zuwa domin kula da lafiyar mutane ta hanyar bayar da magani da kuma matakan kariya, musamman a wuraren da ke da wuyar kaiwa gare su.

Ana kuma wayar da kan mutane game da cututtukan Tarin Fuka, Malariya, hawan jini, cutar suga da tamowa baya ga shirye-shiryen allurar rigakafin domin tabbatar da cewa jarirai da kananan yara sun samu kariya daga cututtuka a-kai-a-kai.

Ba dace a bari cuta da kama mutane ko ta kashe su ba saboda su talakawa ne ko saboda ba za su iya samun kiwaon lafiyar da suke bukata ba.

Shi ya sa gwamnatin jihar ta bullo da inshorar lafiya da nufin rage wa mutane kashe kudade fiye da kima wurin kula da lafiyarsu. Tsarin ya ware kashi 1% na kudaden shigar jihar ga masu rauni kamar tsoffi da talakawa domin tabbatar da samun daidaito a bangaren kula da lafiya.

Sannan ana akwai Shirin Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu da Kananan Yara ’Yan Kasa da Shekaru Biyar Kyauta.

Kadan daga matakan da muka dauka ke nan domin tabbatar da kare hakkin mutane na samun daidaito a bangaren kiwon lafiya.

Kiwon lafiya na kuma samuna idan wasu hakkoki suka samu kamar lafiyayyen ruwan sha da makewayi, lafiyayyen abinci, ingantaccen muhalli da ilimi da kuma amincin wurin neman abinci.

Gwamnati na kokarin ganin cewa su ma wadannan bangarorin an inganta su da nufin inganta lafiyar al’umma.

Wadanne irin rashin daidaito ne manyan kalubale kuke fuskanta wajen samar da kiwon lafiya ba tar da bambanci ba a jihar, sannan wace hanya za ku bi domin magance su?

Wasu daga cikinsu sun hada da bambancin jinsi. Mata sun fi fuskantar barazanar samun kula da lafiya; al’adu sun sa masa sun fi shiga hadarin lafiya, kamar wurin haihuwa; sai sun samu izinin fita zuwa asibiti; rashin karfin aljihunsu da sauransu.

Sannan akwai bambancin da ke tsakanin mazauna karkara da na birane, ta yadda mazauna birane suka fi samun kula da lafiya fiye da kauyuka.

Amma gwamantinmu na kokarin magance wannan matsalar ta tsarin da muka bullo da shi na samar da babbar karamar cibiyar lafiya a kowace mazaba (Ward Focal PHC).

Samar da karin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da manayan asibitoci ko na karkara a dukkannin kananan hukumomi su ma za su taimaka wajen yawaitar wuraren kula da lafiya.

Talauchi shi ma yana kawo irin wannan bambanci kasancewar talauci da rashin ingantacciyen kiwon lafiya suna gogayya ne da juna. Talakawa ba za su iya samun cikakkiyar kula da lafiya, hakan kuman na tasiri wajen tabarbarewar lafiyarsu. Idan kuma suka kashe dan abin da suke da shi, za su shiga talaucin da suke ciki a baya.

Shirin inshorar lafiya da kula da lafiyar mata da kananan yara kyautata, an bullo da su ne domin ganin talkawa da mutane masu rauni na samun kula da lafiya.

Muna kuma kula da mutanen da ke fama da matsalolin lafiya da ke iya jawo tsangwama kamar cutar HIV, Tarin Fuka, matsalar kwakwalwa, da sauransu.

Muna kuma shirin bullo da shirin kula da lafiyar samari da ’yan mata da ba za su iya samun kiwon lafiya ba saboda yanayin da suke ciki, da zimmar rage tsangwama da nuna bambanci a tsakanin mutane.

Akwai sauran aiki, har sai an tabbata kowa, duk matasyinsa, a ko’ina yake, komai talaucinsa yana samun hakkokinsa; Muna kuma aiki haikan wajen magance rashin daidaito ta yadda babu wanda za a bari a baya daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Wajibi ne mu yi aki tare domin magance wadannan matsaloli da wasu abubuwa na nuna bambanci ta yadda kowa sai samu cikakkiyar kula da lafiya mai inganci ba tare da la’akari da shekaru, jinsi, kabila, addini, matsayi, nakasa ko yanayin lafiyarsa ba.