✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu hutu a gareni har sai ’yan Najeriya sun samu saukin rayuwa —Buhari

Ina sane da halin kunci da al’ummar kasar ke ciki, kuma ina aiki tukuru don warware su.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa ba zai huta ba har sai ya kawo musu sauki a kan matsalolin da ke damunsu da suka hada da tsaro da tsadar rayuwa.

Wannan tabbaci da shugaba Buhari ya bayar na cikin sakonsa na taya murnar Sallah ga al’ummar Musulmi da sauran ‘yan kasa.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce yana sane da halin kunci da al’ummar kasar ke ciki, kuma yana aiki tukuru don warware su.

Shugaba Buhari ya bayyana fatan cewa wannan lokaci na Sallah babba, zai kasance silar samun albarka da zaman lafiya da ci gaban ‘yan Najeriya, yana mai bayyana yakinin cewa zamantakewa da kwanciyar hankali za su inganta a kasar.

Shugaban ya shawarci Musulmai da su yi riko da koyarwar addininsu don ganin al’amuransu sun daidaita.

Buhari ya tafi Daura hutun Sallah

A Yammacin Juma’ar nan ce Buhari ya isa garin Daura da ke Jihar Katsina domin yin bikin Babbar Sallah.

Shugaba Buhari ya samu tarba daga Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk da wasu sarakunan gargajiya.

Buhari ya isa Daura ne kwanaki uku bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocinsa a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

An kai harin ne kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an da ke yi wa shugaban hidima da kuma ’yan jarida, a cewar sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar.

Sai dai an yi sa’a Shugaba Buhari ba ya cikin ayarin kamar yadda sanarwar ta bayyana.