✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu maganar sulhu tsakanina da Ganduje — Kwankwaso

Kwankwaso ya ce babu wata maganar sulhu tsakaninsa da Ganduje.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta batun tattaunawar sulhu da aka ce yana yi da Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, inda ya ce ya ji dadin ziyarar ta’aziyyar da Gwamnan ya kai masa ta rasuwar kaninsa.

Sai dai ya kore yiwuwar bawa Ganduje damar samun wani matsayi ko mukami idan damar hakan ta samu ta bangarensa.

Ya ce ‘“A yanzu dai ka san ba a jam’iyya daya muke ba, don haka ina ganin babu ma bukatar yin wannan tambaya, don haka ko da dama ta samu akwai mutanen da suka cancanta cikin wadanda nake tare da su”.

A makon da ya wuce Kwankwaso ya musanta rade-radin da ake na cewar yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP tare da shirin sauya sheka zuwa APC, wanda hakan ya zama batun tattaunawa na tsawon lokaci a kafafen watsa labarai.

Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya yi tsamari tun bayan 2015 bayan Gwamnan Kano na yanzu ya dare kan kujerar mulkin Jihar.

Sai dai a baya-bayan Ganduje ya nuna cewar akwai yiwuwar yin sulhu da tsohon uban gidan nasa a siyasa, wanda ya ce tun asali wasu ne suka shiga tsakaninsu.

Har wa yau, Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta APC tsakaninsa da tsagin tawagar tsohon Gwamna kuma Sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau.

Rikicin ya sanya bangaren Gwamnan rasa shugabancin jam’iyyar APC daga hannun shugabanta, Abdullahi Abbas a kotu, wanda Haruna Abdullahi Zago ya yi.