✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu mahalukin da zai sa APC a aljihunsa —Buhari

Buhari ya ce babu wanda zai zauna a Legas ya tilasta wa APC kan dan takara.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu wani dan Adam da ya isa ya tilasta wa jam’iyyar APC yin yadda yake so wajen tsayar da dan takara.

Buhari ya jaddada cewa daukacin ’ya’yan jam’iyyar ne ke da alhakin yin alkalanci kan yankin da za a ba wa takara.

“Ba wanda ya isa ya ce zai zauna a Legas ya zaba wa jam’iyyar yankin da za ta fitar da takara, alal misali.

“Nan gaba za a yi babban taron jam’iyya, kuma babu wani dan jam’iyyar da za a bari ya yi wa muradunta yadda ya ga dama,” inji shi.

A wata hira ta musamman da gidan Talabijin na Arise TV ya yi da shi ranar Alhamis, Buhari ya ce APC na yin gyare-gyare domin tafiya da kowane dan jam’iyyar.

“An fara sauye-sauye daga kasa zuwa sama ta hanyar sabunta rajista, saboda dole ne a yi tafiyar tare da kowane dan jam’iyya.

“Abin da ya kamata shi ne jam’iyyar ta san yawan mambobinta a kowace jiha,” a cewarsa.

Buhari ya kara da cewa, “Gamnatin APC ta samu nasarori da dama, idan aka kwatanta da yanayin da ake ciki kafin zuwanmu da yanzu za a gani.”