✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu mai hankalin da zai sake zaben APC a 2023 —Sanata Binos

Sanata Binos Dauda ya ce babu dan Najeriya mai cikakken hankali da zai sake zaben APC a 2023

Babu wani mai cikakken hankalin da zai sake zaben Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa na shekarar 2023 a cewar Sanata Binos Dauda.

Sanata Binos, mai wakiltar Adamawa ta Kudu a karkashin Jam’iyyar PDP ya ce ’yan Najeriya za su yi watsi da APC a zaben 2023 ne saboda yadda jam’iyyar ta jefa su cikin wahalhalu.

Dan Majalisar Dattijan ya fadi haka ne a yayin da yake raba kayayyakin noma ga manoman Karamar Hukumar Belwa ta Jihar Adamawa.

Binos ya ce alkaluma na nuna cewa zaben da aka yi wa jam’iyyar APC a shekarar 2015 ba karamin kuskure ba ne, ganin halin da jefa ta kasar Najeriya a ciki.

“Ku duba farashin Dala a 2015 da kuma farashinta a yanzu, haka kuma farashin kayayyakin bukatun yau da kullum….

“A bangaren tsaro, shekarar 2015 da yanzu fa? …A ina ne ake zaman lafiya,” in ji dan majalisar.

Ya kuma zargi gwamnatin APC da kawo canji mara amfani ga ’yan kasa da kuma rashin iya mulki da  rashin sanin ya kamata.