✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu matsala tsakanina da Goje —Gwamna Inuwa

Gwamnan ya ce dole ne kowa ya bi tsarin da jam'iyya ta zo da shi.

Rikicin cikin gida da ya bullo a jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe tsakanin magoya bayan Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da uban gidansa Sanata Danjuma Goje ya so raba jam’iyyar gida biyu.

Sai dai kuma Gwamnan ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ba shi da wata matsala da tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje.

Rikicin nasu ya samo asali ne kan wane ne jagoran jam’iyyar APC a Jihar, inda Sanata Goje yake ganin shi ne jagora, gwamnan kuma yake ganin shi ne ya fi dacewa ya zama a wannan matsayi.

“Babu wata matsala a tsakaninmu, jam’iyya ce take da hakkin ba wa kowa dama na kasancewa yadda zai zama” inji gwamna Inuwa.

Ya kara da cewa dukkansu ’ya’yan jam’iyyar ne kuma dole a bi tsarin da jam’iyya ta zo da shi.

“Idan na yi ba daidai ba a jam’iyya a taru a dawo da ni kan hanya, haka ma duk wanda ya yi ba daidai ba, shi ma a dawo da shi ya bi daidai” a cewarsa.