✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Babu mai yi wa Buhari katsa-landan a mulkinsa — Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban ta musanta cewar akwai masu juya wa Buhari tunani

Fadar Shugaban Kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ke daukar kowanne irin mataki a kashin kansa, ba tare da wani ya tilasta shi ko ya yi masa katsa-landan ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata.

Kazalika, sanarwar ta ce, “Shugaba Buhari na daukar matakansa ne kuma ya aiwatar da su ba tare da wasu da ake wa kallon ’yan hana-ruwa gudu ba sun tsoma masa baki.”

Sanarwar na zuwa ne bayan da ake rade-radi a kafafen yada labarai cewar wasu na yin uwa da makarbiya a gwamnatin Shugaba Buhari.

Hakan ne ma a cewarsu ya sa har ya gaza zabar magajinsa a zaben fid-da gwanin Shugaban Kasa da jam’iyyar APC ta kammala.

Har wa yau, Fadar ta ce irin yadda aka gudanar da zaben na fid-da-gwanin dan takarar Shugaban Kasa a APC, ya nuna cewa Buhari Shugaba ne mai martaba dimokuradiyya duk da cewar shi tsohon soja ne.