✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu sunan Ahmad Lawan da Akpabio a ’yan takarar sanata —INEC

INEC ta musanta sanya sunan Lawan da Akpabio a matsayin ’yan takarar Sanata a zaben 2023

Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta jadadda cewa ba ta karbi sunan Shugaban Majalisar Dattawa ba, Sanata Ahmad Lawan da tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio a matsayin ’yan takarar Sanata ba.

INEC ta ce ta yi kememe wajen karbar sunan Ahmad Lawa a matsayin ’yan takarar Yobe ta Arewa ko Akpabio a matsayin dan takarar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma sakamakon takaddamar da ke tattare da zaben fidda-gwanin da aka yi na jam’iyyarsu ta APC.

INEC t musanta rahotannin da yadawa cewar ta musanya ainahin sunayen ‘yan takarar da jam’iyyu suka aike mata a matsayin ‘yan takarar Sanatocin.

Kwamishinan Sadarwa da Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye, ya sanar cewa, “Domin fayyacewa takardar EC9 (ta mika sunayen ’yan takara da jam’iyyu suka yi) ita ce jam’iyyu suka sanya a shafin INEC na karbar sunayen ’yan takarar da suka zaba.

“Wannan na rubuce karara a saman takardar wadda aka karba ranar 17 ga watan Yuni na 2022 a lokacin da aka rufe shafi.

“Abin da ya biyo bayan mako daya shi ne wallafa bayanan takardun ’yan takarar da aka zaba, inda hukumar ba ta wallafa bayanan takardun mutanen biyu ba da ake magana a kai ba.”

Sannan ta kara da cewa, “Abin da hukumar ta yi ya janyo matakin shari’a wadda har yanzu ake yi.

“Saboda haka abu ne da ya saba hankali a je a mika wata takarda ta daban da aka yi wa sauye-sauye cewa an yarda da mutum biyun a matsayin ’yan takara yayin da maganar ke gaban shari’ar.”

Idan ba a manta ba, Sanata Ahmad Lawan wanda ya shiga neman takarar shugaban kasa a APC ya fadi zaben fidda-gwanin a hannun Bola Ahmed Tinubu.

A bangare guda kuma Bashir Machina ya lashe zaben fidda-gwani na kujerar Sanatan da shugaban majalisar ke wakilta.