✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu tabbacin ba za a iya yi wa rumbun adana bayanan INEC kutse ba – Jega

Ya ce matakin takaita ta'ammali da tsabar kudi a wannan lokaci ragon azance ne

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya ce abu ne mai yiwuwa a iya yin kutse cikin rumbun adana bayanan hukumar.

Duk da kyakkywan shirin da INEC ta ce ta yi wa zaben na 2023, Jega ya ce ba shi da tabbacin cewar  ma’adanar bayanan INEC ta tsira daga sharrin masu kutse.

“A wannan zamani, babu wanda ke da garanti 100 bisa 100 cewa ba za a iya yi wa matattarar bayanan kutse ba, sai dai in ba a intanet take ba.

“Da muka gudanar da zabe a 2015 matattarar bayananmu ba a intanet take ba. Amma yanzu, musamman da ya zamana ta intanet za a tattara sakamako, dole za a yi amfani da intanet,” in ji shi.

Jega ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar talabijin din Trust TV game da shirye-shiryen INEC dangane da zaben da zai gudana ranar Asabar.

A cewarsa, “A fadin duniya, ana amfani da matattarar bayanai ta intanet kuma cikin nasara, saboda akan yi amfani da tsarin tsaron kare bayanai a intanet.”

Ya kara da cewa INEC ta ba da tabbacin daukar ingantaccen mataki wajen  kare rumbun tattara bayananta a intanet musamman daga lalatar masu kutse.

Da yake tsokaci kan na’urar BVAS da INEC ta shirya yin amfani da shi a zabukan 2023, Jega ya yaba da ingancin na’urar.

INEC ta shirya gudanar da zaben 2023 ta yin amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu kada kuri’a don samun sahihin zabe.

BVAS na’ura ce wadda aka samar da ita musamman domin tantance Katin Zabe a lokacin zabe.

A hannu guda, Jega ya bayyana tsarin takaita hada-hadar tsabar kudi a kasa da gwamnati ta dauka a matsayin ragon azanci.

Ya ce ba daidai ba ne daukar  irin wannan mataki a lokacin babban zabe kamar wannan.

“A fahimtata, akwai bukatar tsabar kudi, saboda lokacin zaben 2015, ma’aikatan wucin-gadi 750,000 muka tura.

“Kuma wannan rukunin ma’aikata ne da ake bukatar su kwana a wuraren da ake kira Cibiyoyin Mazabu (RAC).

“Wadannan ma’aikata suna bukatar kudi domin ba lallai ne a samu na’urar ATM ko POS don cire kudi a inda aka tura su ba,” in ji Jega.