Babu tabbacin kwanan watan haihuwar Annabi (SAW) —Sheikh Gumi | Aminiya

Babu tabbacin kwanan watan haihuwar Annabi (SAW) —Sheikh Gumi

Dokta Ahmad Abubakar Gumi
Dokta Ahmad Abubakar Gumi
    Abdullahi Abubakar Umar

A yayin da al’ummar Musulmi ke tsaka da murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) na wannan shekara, Sheikh Dokta  Ahmad Abubakar Gumi ya ce babu tabbaci game da ainihin kwanan watan haihuwar Annabin. 

Da yake magana game da kwanan watan haihuwar Annabi Muhammad (SAW), malamin ya ce an haife shi ne a lokacin jahiliya, kuma a lokacin Larabawa ba su rubutu ko karatu, kamar yadda ya zo a cikin da Hadisin Umar (RA).

Hadisin da aka ruwaito daga Umar (RA) ya ce: “Mun kasance al’umma da ba mu iya karatu ko kirge ba. Kwanan wata haka ne ko haka — wato wani lokaci wata ya yi kwana 29, wani lokacin kuma ya yi kwana 30.”

Bugu da kari, ya ce ita kanta kalandar Musulinci da ake amfani da ita yanzu a lokacin khalifancin Sayyadina Umar aka fara amfani da ita.

Mashahurin malamin ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar da ake tsaka da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyyayyen Halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Shehin Malamin ya kawo dalilai daga Al-Kur’ani da hadisai da ma littafin Linjila, cewa tun daga kan Annabi Adam (AS) har zuwa kan Annabi Muhammad (SAW) babu wani annabi da tarihin kwanan watan haihuwarsa ya inganta.

“Babu wani Annabi, tun daga Annabi Adam (AS) har zuwa Annabi Muhammad (SAW), da ake da tabbacin ainihin kwanan watwan haihuwarsa.

“Duk kiyastawa aka yi saboda a lokacin babu wani kundin adana bayanan haihuwa domin ba a dauki hakan da muhimmanci ba kamar yanzu,” inji malamin.

Ya bayyana cewa addini na gaskiya yana kasance ne bisa hujjoji ba kintace da hasashe ko zato ba.

Ya kafa hujja da Al-Kur’ani cewa: “Yawancinsu babu abin da suke bi face zato: Tabbas zato ba ya wadatarwa da komai daga gaskiya. Hakika Allah mai cikakken sani ne game da abin da suke aikatawa.” (Suratu Yunus, aya ta 36).

– Ranar haihuwar Annabi Adam da Isah (AS)

Sheikh Gumi ya ce Annabi Adamu (AS), a addinin Musulunci da Kirista an yi ittifakin cewa an halicce ne a ranar Juma’a da yamma, amma babu wanda ya san kwanan watan.

Ya ci gaba da cewa Annabi Isah (AS) da Kiristoci ke bikin haihuwar sa a shekarata 12BC, babu wata hujja daga cikin littafin Linjila a kan haka, shi ya sa wasu daga cikin Kiristoci ba su yi imani da bikin Kirsimati a matsayin ranar da aka haife shi ba.

Daga karshe malamin ya bayyana cewa bukukuwan Kirsimeti da na Maulidi kagaggun abubuwa ne a addinan guda biyu.