✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Babu tabbas za a yi jarabawar Mayu/Yuni a 2021 —WAEC

WAEC ta ce nan gaba za a sanar da lokacin da zai dace na jarabawar

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta ce babu tabbacin gudanar da jarabawar da ta tsara yi a watannin Mayu da Yuni a bana.

Babban Jami’in WAEC na Najeriya, Patrick Areghan, ne ya bayyana haka a lokacin da yake sanar da sakamakon jarabawar da dalibai masu zaman kansu suka rubuta na tsakanin 15 ga Fabrairu zuwa 11 ga Maris 2021.

Patrick Areghan, bayyana a ranar Talata cewa kasancewar bangaren ilimi bai gama farfadowa daga illar da bullar COVID-19 ta yi masa ba, baya ga rikita jadawalin karatu, da wuya a iya gudanar da jarabawar yadda aka tsara tun da farko.

“Ina amfani da wannan damar domin karyata masu baza rade-radi game da jarabawar WASSCE ta 2021.

“Har yanzu bangaren ilimi bai gama murmurewa daga illar da COVID-19 ya yi masa ba, tare da illata jadawalin karatu a fadin Najeriya.

“Saboda haka da wuya a iya gudanar da jarabawar a watannin May da Yuni na bana. Nan gaba za a sanar da lokacin da zai dace ga kasashe da dama.

“Saboda haka ana shawartar dukkanin masu ruwa da tsaki da su ci gaba da jira har zuwa lokacin da za su ji daga WAEC,’’ inji Areghan.

Sai dai ya kara da kira ga Shugabannin Makarantu da su ci gaba kiyaye wa’adin da WAEC ta sanya na yin rajistar dalibai domin jarabawar da ke tafe.

“Ana shawartar daukacin makarantu da su kiyaye ka’idojin yin rajista saboda kar a samu wata tangarda,’’ kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma shawarce su da mayar da hankali wajen yi wa dalibansu gwaji da kuma tara sakamakon daliban.