Daily Trust Aminiya - ‘Babu wanda cutar Coronavirus ta kashe tsawon kwana tara a N
Subscribe

Wani jami’in kiwon lafiya yana daukar samfur a daya daga cikin cibiyoyin da aka kafa da taimakon NCDC a wasu al’ummun Yankin Babban Birnin Tarayya

‘Babu wanda cutar Coronavirus ta kashe tsawon kwana tara a Najeriya’

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC, sun nuna cewa ya zuwa yanzu an kwashe kwanaki 9 ba tare da samun wanda cutar ta kashe ba a duk fadin kasar.

NCDC ta sanar da hakan ne ranar Talata cikin taskar bayanan da saba fitar wa game da cutar duk rana.

A yanzu jimillar mutum 2,061 cutar ta kashe a duk fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a ranar 27 ga watan Fabrairun bara.

Kazalika, bayanan da NCDC ta fitar a jiya sun nuna an samu karin mutum 120 sabbin kamuwa da cutar cikin jihohi bakwai da kuma birnin Tarayya Abuja.

Sabbin kamuwar sun fito ne daga Jihar Enugu mai mutum 53, sai Legas da mutum 22 yayin da aka samu karin mutum 18 a Ribas.

Jihar Ogun na da mutum takwas, Abuja mutum bakwai, sai kuma jihar Abiya da Kano inda aka samu mutum shida-shida da kuma daya a Jihar Jigawa.

NCDC ta ce mutum 1,870,915 aka yi wa gwajin cutar a duk fadin kasar, inda adadin wadanda aka samu sun harbi ya tuke a mutum 164,423.

More Stories