✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu wanda ya fi shiga matsalar tsaro kamar manoma’

Don haka dole farashin kayan amfanin gona ya yi ta tashi sama.

Wani babban manomi kuma Shugaban Kungiyar Noma Don Riba na garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, Alhaji Tasi’u Bako Nabawa ya bayyana cewa yanzu a Najeriya babu wanda yake cikin barazanar matsalar rashin tsaro da ya kai kamar manoma.

Manomin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya.

Nabawa ya ce, duk wanda ya dubi halin da ake ciki a Najeriya idan farashin kayan amfanin gona ya tashi sama ba abin mamaki ba ne, saboda manoma sun shiga cikin barazana ta rashin tsaro a kasar nan.

Ya kara da cewa, kowa ya sani duk wata mu’amalar noma ana yinta ne a bayan gari, kuma halin matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya, yanzu zuwa bayan gari ya zama matsala.

Saboda yadda ake sace-sacen mutane da manoma a gonaki ana garkuwa da su sai an biya kudin fansa kafin a sake su. Don haka dole ne farashin amfanin gona ya tashi sama a Najeriya.

“Gaskiya yadda farashin kayan amfanin gona yake tashi sama a bana akwai abin tsoro. Saboda duk kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, kamar Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana sun dogara da kayan amfanin gonar da ake nomawa ne a Najeriya, musamman a yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna.

“Domin yanzu idan ka zo kasuwannin wannan yanki, za ka ga mutanen wadannan kasashe suna ta sayen kayan amfanin gona suna fita da shi.

“Don haka dole farashin kayan amfanin gona ya yi ta tashi sama.”

Manomin ya yi kira ga manoman da suka samu damar yin noma a bana, su yi taka-tsantsan da sayar da kayan amfanin gonar da suka noma.

Domin burin duk wani manomi ne idan ya yi noma a bana a badi ma ya kara yin noman.

Ya ce, idan manoma ba su yi hattara ba sun yi tanadi ba, manomin da ya noma buhu 50 a bana, zai yi wuya ya iya noma buhu 25 idan aka dubi halin da ake ciki a kasar nan.

Ya yi kira ga gwamnati ta rika kiran manoma na gaskiya idan ta tashi tallafa wa manoma.

Domin sau tari idan gwamnati ta tashi tallafa wa manoma tana kiran manoma ne na bogi, maimakon manoma na gaskiya.