✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda ya isa ya fille min kai kan ‘dokar zaben Buhari’ —Buba Galadima

Tsuguno ba ta kare ba, Buhari na neman a cire sashen da bai yi masa ba daga sabuwar dokar.

Babban mai adawa da Shugaban Kasa Muhammadu Burahi kuma tsohon dan a-mutunsa, Injiniya Buba Galadima, ya ce babu wanda ya isa ya fille masa kai, duk da cewa Buhari ya sanya hannu a kan sabuwar dokar zabe.

A baya Injiniya Buba Galadima ya ce Buhari ba zai taba rattaba hannu a kan sabuwar dokar zaben ba, yana mai cewa idan har Buhari ya sanya mata hannu a kan dokar, to shi ya amince a fille masa kai.

Sai dai kuma, bayan Buharin ya sanya wa dokar hannu, Buba Galadima ya ce ya yi amannar cewa ba da zuciya daya Buharin ya sanya hannu a kan dokar ba, don haka da sauran rina a kaba.

Ya kara da cewa tun ba a je ko’ina ba, Buhari yan fara neman cire wasu sassa da ba ya so daga sabuwar dokar da ya dade yana kauce-kaucen sanya mata hannu.

Wani masanin kuma mai bibiyar dokokin zaben Najeriya, Aminu Tanimu Abdullahi, ya ce sabuwar dokar, wadda ta halasta tura sakamakon zabe ta intanet, zai taimaka wajen dakile magudin zabe.

Sai dai kuma wasu na ganin tura sakamakon zabe ta intanet ba zai hana magudin zabe be, domin masu kutse ta intanet suna iya yin kutse su sauya alkaluman kafin a kai ga sanar da sakamako.

‘Da sauran magana’

Masu bibiya da masana harkar siyasa da masu sharhinta na ganin bukatar Buhari ta yin gyara ga sabuwar dokar zaben, kasa da kwana 10 bayan ya rattaba hannu a kai alama ce da ke nuna tsuguno ba ta kare ba.

Sun danganta hakan ne da buktar da Buhari ya aike wa Majalisar Dokoki na neman cire shashe na 84 na dokar, wanda ya haramta wa ministoci da sauran masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ko zaben ’yan takara.

Buhari na ganin sashen ya ci karo da kundin tsarin mulki, saboda ya wajabta wa masu irin wadancan mukaman ajiye aikinsu kafin su iya tsayawa takara ko zaben ’yan takara.

A ranar Talata dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisa bukatarsa ta neman soke sashen na 84, wanda ya haramta wa wa ministoci da sauran masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ko yin zaben ’yan takara ba tare da sun ajiye mukamansu ba.

Wani masanin kimiyyar siyasa, Dokta Farouk BB Farouk, ya ce majalisar na da hurumin soke sashen ko kuma barin dokar a yadda take, amma bisa fahimtar juna tsakaninta da bangaren zartarwa.

Ja-in-ja kan sabuwar dokar zabe

Tun a shekarar 2019 dai ake ta kai ruwa rana a kan sabuwar dokar zaben, tsakanin Majalisar Dokoki ta Kasa da bangaren Shuaban Kasa, inda akalla sau hudu Majalisar tana mika wa shugaban kasa, yana kin amincewa.

Kin amincewa da dokar da Buhari ya yi a baya sakamakon wasu kura-kurai da ya ce dokar ta kunsa, ta haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin bangarorin biyu.

Daga baya har majalisar ta fara yunkurin yin gaban kanta wajen aiwatar da dokar.

Kungiyoyin fafutika sun ba wa shugaban kasa wa’adin kwanaki ya sanya hannu a kan dokar, idan ba haka, za su kaddamar da wata gagarumwar zanga-zanga a fadin Najeriya.