✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu wanda ya isa ya yi babakere a shugabancin Najeriya’

Najeriya ta kowa ce kuma babu wanda zai kori wani daga kasar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya bayyana cewa babu wani bangare na mutane komai bangarancinsa na addini ko kabila da ya isa ya yi babakere ga shugabancin kasar nan.

Tambuwal ya bayyana hakan yayin da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Rabaran Ayokunle Samson Olasupo ya kai ziyara fadarsa da ke birnin Shehu.

A cewarsa, “Shugabancin kasar nan na taimakon juna ne saboda haka Najeriya ta kowa ce kuma babu wanda zai kori wani daga kasar.

“Saboda haka a yanzu akwai bukatar ci gaba da zaman tare domin ci gaban kasa.

A kan haka ne Tambuwal ya nanata cewa, irin shugabanci da kasar nan ke bukata shi ne wanda zai fahimci duk wasu batutuwa masu janyo rarrabuwar kai ta hanyar tsarin gudanar da mulki ba tare da nuna kabilanci ko bambancin addini ba.

A nasa bangaren, Olasupo y ace ya kai ziyara Sakkwato ce domin tattaunawa da Sarkin Musulmi da kuma mutanen Jihar domin gano bakin zaren yadda za a magance matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar baki daya.

Kazalika, ya jajanta wa al’ummar jihar kan mutanen da aka kashe a hare-haren ’yan bindiga tare da kwadaitar da su a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista.