✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda ya lashe zaben Shugaban Najeriya na 2023 – Mataimakin Peter Obi

Mataimakin na Peter Obi, ya ce babu wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi.

Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed, ya ce babu dan takarar da ya lashe zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Baba-Ahmed, ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan zaben Shugaban Kasa a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

A ranar Laraba, 1 ga watan Maris ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben Shugaban Kasa.

Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, wanda ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar LP, ya samu kuri’u 6,101,533, sai Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da ya samu kuri’u 1,496,687.

Sai dai jam’iyyar PDP da LP sun yi watsi da sakamakon zaben, inda suka garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu.

Sai dai a yayin hirar, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP, ya ce Tinubu bai cika sharuddan da ake bukata na a ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa ba.

“Tinubu bai cika sharuddan ayyana zababben shugaban kasa ba. Don haka a yanzu babu wani shugaban kasa da aka zaba a Najeriya domin wanda aka ayyana ya saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.”