Babu wani abu da gwamnoni za su iya kan matsalar tsaro— Ishaku | Aminiya

Babu wani abu da gwamnoni za su iya kan matsalar tsaro— Ishaku

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku
Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku
    Ishaq Isma’il Musa, Rejoice Iliya

Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba ya ce duk gwamnonin Najeriya babu yadda suka iya da matsalar kashe-kashe da ke addabar al’umma a kasar nan.

Haka kuma Ishaku ya ce babu wani taimako da gwamnonin kasar ke samun wajen tsare rayukan al’umma da dukiyoyi a jihohin kasar.

Darius ya yi wannan jawabi ne biyo bayan harin da mayakan Ambazoniya daga Kamaru suka kai wani kauye a Jihar Taraba inda suka kashe mutum 11 ciki har da Basarake.

A cewarsa, babu wani katabus da gwamnatinsa za ta iya na hana aukuwar ire-iren wadannan hare-hare la’akari da cewa ba shi da iko a kan hukumomin da sha’nin tsaro ya rataya a wuyansu.

Gwamnan ya ce tun gabanin aukuwar harin ya kai wa Gwamnatin Tarayya da Dakarun Soji korafi domin ankarar da su kan barazanar da jiharsa ke fuskanta daga mayakan da suka tsallako daga Kamaru.

A hirar da ya yi a cikin Shirin Siyasar Yau da Gidan Talabijin na Channels, Gwamna Darius ya ce da a ce yana da iko a kan ’yan sanda, da kuwa ya jibge su a yankunan da suke fuskantar barazanar tsaro a jiharsa, lamarin da ya sanya ya sake jaddada bukatar samar da ’yan sandan jihohi a fadin kasar.

“Muna karkashin ikon Gwamnatin Tarayya idan aka zo batun sojoji da ’yan sanda, babu abin da gwamnatin jiha za ta iya domin a kansu muka dogara.

’Saboda haka babu wani abu da wani gwamna zai iya yi a kan lamarin. Ku je ku tambayi duk gwamnonin kasar nan, duk mun rajaa ne a kan taimakon Gwamnatin Tarayya.

“Wannan kalubale ba ni kadai nake fama da shi ba, duk gwamnonin Najeriya babu yadda suka iya, kuma wannan ba shi ne karon fari da nake fadin haka ba.

“Haka kuma ba ni kadai ba ne nake fama da rashin samun taimako wajen magance matsalar tsaro, duk gwamnonin Najeriya na wannan korafi, wanda haka ya sa muke neman a samar man da yan sandan jihohi,” in ji Darius.

Dangane da batun ko akwai wata hanya da yake ganin za a yi ribata domin magance matsalar tsaro, Gwamnan ya ce “muna da ’yan sa-kai, amma me dan sa-kai zai iya idan ba shi da bindiga kirar AK-47, kuma wadansu na kawo masa hari da ita.

“Wannan shi ne babatun da nake yi, ko Ma’aikatan Hukumar Shige da Fice sun yi iyaka bakin kokarinsu wajen hana mayakan Ambazoniya shigowa yankunanmu, amma ban san irin bindigogin da suke amfani da su ba, watakila ma irin tsofaffin bindigogin nan ne na toka da idan an yi harbi daya sai a noke.

“Maganar gaskiya ita ce su kansu sojoji da ’yan sandan kasar nan suna bukatar a wadata su da ingatattun makamai masu tafiya da zamani.”

Rahotanni sun bayyana cewa, a Larabar da ta gabata ce mayakan Ambazoniya suka yi wa Kauyen Manga na Karamar Hukumar dirar mikiya, inda suka kashe mutum 11 ciki har da Hakimin kauyen.