✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wani jirginmu da ya yi hadari — ’Yan sanda

Babu wanda ya samu rauni a mutanen da ke cikin jirgin.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da aka rika yayata cewa wani jirgi mai saukar ungulu mallakarta ya yi hatsari a Bauchi.

Rundunar ta kuma musanta labaran da ke cewa wadanda suke cikin jirgin sun samu munanan raunuka.

Rundunar ta ce jirgin wanda ya taso daga Abuja a ranar 26 ga watan Janairun 2022 ya yi saukar gaggawa ne a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Rundunar ta ce duka mutane shida da ke cikin jirgin lafiyarsu kalau haka kuma rundunar ta ce direban jirgin kwararre ne wanda a dalilin haka ne ya sa ya sauka lafiya ba tare da jirgin ya yi dameji sosai ba.

Rundunar ta ce farfelar jirgin ta baya ce kawai ta samu matsala a yayin sauka.

Tun da farko dai gidan rediyon gwamnatin tarayyar Najeriya ya ruwaito Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama ta kasar, AIB tana tabbatar da labarin.