✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu yarjejeniyar Buhari zai mika wa Tinubu mulki a 2023 – Okechukwu

Ya ce sam Buhari ba ya kulla irin wannan yarjejeniyar da kowa.

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki kuma Babban Daraktan Muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya ce babu wata yarjejeniya tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jagoran jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu kan mika mulki a 2023.

A wata tattaunawarsa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Mista Okechukwu ya ce ba kasafai ma Buhari yake kulla irin wannan yarjejeniyar da mutane ba.

“A matsayina na mamba a tsohuwar jam’iyyar APC, ban taba jin irin wannan yarjejeniyar ba, kuma abu mafi muhimmanci ma shine Buhari ba zai so, ko ma in ce ba ya shiga kowacce irin yarjejeniya ko rubutacciya ko kuma ta baki da kowa. Amma dai in aka yi masa abin alheri yana yabawa.

“Abin da kawai na sani shi ne da tuni Tinubu ne ya zama Mataimakin Shugaban Kasa a 2015 in ba dan tarnakin da ya fuskanta ba, sakamakon gargadin da muka yi a kan illar ba da takara ga Musulmai biyu.

“A lokacin, mun ce musu irin yadda tsarin Abiyola da Kingibe na Musulmai biyu ya yi aiki a 1993 ba lallai ne ya yi ba a 2015, idan Buhari da Tinubu suka yi takara, saboda yanayin ya banbanta.

“Abin da ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo ya maye gurbinsa a wancan lokacin kenan,” inji Okechekwu.

Da aka tambaye shi kan matakin da jam’iyyar ta dauka na fitar da dan takarar Shugaban Kasa ta hanyar maslaha a 2023, sai ya ce, “Da farko dai yana da kyau mu san cewa Buhari ba zai sake takara a karo na uku ba.

“Na biyu kuma, a irin nawa tunanin, bana jin kowanne kwamiti da za a dora wa alhakin wannan zai cire jagoranmu, Bola Tinubu daga fafatawar.

“Ni ina ganin ma zai kasance daga cikin na gaba-gaba daga jerin ’yan takarar da za su tsaya, la’akari da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar har APC ta kai ga gaci a 2015,” inji shi.

A kwanakin baya ne dai tshohon shugaban tsohuwar jam’iyyar CPC, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce akwao yarjejeniyar cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubun in ya kammala wa’adinsa na biyu a 2023.

Hakan, a cewar Sanata Hanga shi ne ma ya hana Tinubun ficewa daga APC bayan kammala wa’adin farko na Shugaba Buhari.