✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bacewar dan kamfan mata ya kashe aure

Wata kotu da ke zamanta a Mapo na Ibadan ta raba auren wata mata Sadiya Abbas da mijinta Azeez bisa batan dan kamfanta. Sadiya ta…

Wata kotu da ke zamanta a Mapo na Ibadan ta raba auren wata mata Sadiya Abbas da mijinta Azeez bisa batan dan kamfanta.

Sadiya ta shigar da karar neman kotun ta kawo karshen aurensu bisa zargin mijin nata da sace dan kamfanta domin yin tsafi.

Ta shaida wa alkalin kotun, Ademola Odunade cewa tana fargabar cutuwar rayuwarta in ta ci gaba da zama a matsayin matarsa.

‘Ban taba jin dadin zama da shi ba’

Ta ce, “Ban taba jin dadin auren ba. A lokacin da musgunawar da yake min ta kai kololuwa kwatsam sai na nemi dan kamfaina na rasa. Shi kuma ya ce wai bai gan shi ba.

“Bayan kwana uku kuma sai na gan dan kamfan a inda na duba ban gani ba, daga nan ne na gane muguwar aniyarsa a kai na.

“Allah Ne kadai Ya san abin da zai faru da ni, gaskiya na gaji da zama da shi. Tun daga ranar da na aure shi ba wani jin dadi.

“Hatta lokacin da nake da juna biyu babu wata kulawa da ya nuna min. Duk da hakan kuma wasu lokutan yakan yi kokarin yi min fyade, gaba daya ya bi ya sa min ido”, inji Sadiya.

‘Ita ce sanadiyyar cinye jari na’

Sai dai Azeez ya musanta zarge-zargen inda ya ce hasali ma ita ke kokarin jefa shi cikin kangin bashi.

“Sam Sadiya ba ta yi min fatan alheri; duk jarin kasuwancina a kanta ya ke karewa.

“Karshen abin ma wata ran sai tsakar dare take dawowa gida wanda hakan har karatun ’ya’yanmu ya shafa saboda suna barci a aji in sun je makaranta.

“Mafi yawan lokuta sai dai in sayi abinci saboda ba ta girkawa, ga yawan korafi akai-akai ko ma ta kwashe kayanta ta bar gidanta.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Ademola ya ce babu sauran soyayya tsakanin ma’auratan saboda haka ya sanar da katse igiyar auren nan take.

Daga nan sai ya umarci matar da ta ci gaba da rike ’ya’yan da suka haifa guda daya tare da umartar mijin ya rika biyan N5,000 a kowane wata baya ga daukar sauran dawainiyarsa.