✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakala: An Daure Tsohon Shugaban Jami’a Shekaru 35

Wata Babbar Kotun Tarayya ta daure tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Magaji Garba shekaru 35 kan laifin almundahanar Naira miliyan 260.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta daure tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Magaji Garba shekaru 35 kan laifin almundahanar Naira miliyan 260.

Alkalin kotun da ke Garki a Abuja, Maryam Hassan Aliyu, ce ta yanke hukuncin, bayan samun sa da aikata laifuka biyar na almundahanar da aka tuhume shi da su.

Kakakin Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Wilson Uwajaren, ya bayyana wa Aminiya cewa an kamo tsohon shugaban jami’ar ne a ranar 12 ga watan Oktoba, 2021, bisa zargin karbar wasu makudan kudade daga hannun wani dan kwangila da zummar zai ba shi kwangilar Naira biliyan uku don katange jami’ar.

Uwajeran ya ce hakan ya saba wa sashi na 1 (1) (a), da sashi na 1 (3) na Dokar Zamba da Dangoginta ta 2006.

Da fari wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai bayan gabatar da takardu da shaidu da EFCC ta yi a gaban kotun, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 35.

Hukuncin da aka yanke masa ya hada da daurin shekaru bakwai ba tare da zabin biyan tara ba a kan kowanne daga laifuka uku na farko, da kuma daurin shekaru bakwai  kan laifi na 4 da 5 tare da zabin biyan tarar Naira miliyan 10 kowanne.