✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Badakalar fansho: Maina ya sake sumewa a kotu

Abdulrasheed Maina ya sake yanke jiki ya fadi a gaban Babbar Kotun Tarayya

Tsohon Shugaban Hukumar Gyaran Fansho ta kasa (PRTT), Abdulrasheed Maina ya yanke jiki ya fadi a kora na biyu a gaban kotu.

Maina ya fadi ne a lokacin da kotu ke ci gaba da sauraron shari’ar zarginsa da karkatar da Naira biliyan biyu na kudin fansho a lokacin da yake shugabancin PRTT.

Ya fadi a sume ne a lokacin da lauyansa, Anayo Adibe yake yin jawabi  a gaban Mai Shari’a Okon Abang da ke sauraron shari’ar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Lauyan na neman kotun ta dage zaman don ya yi nazarin zamanta na baya kafin ya shigar da bukatar watsi da zargin da ake wa wanda yake karewa.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Maina wanda take tuhumar sa da laifuka 12 na karkatar da kudaden fansho.

Sumewar tasa ta tilasta kotun ta dakadar da zaman na ranar Alhamis domin jami’an gidan yari da danginsa su duba shi.

 

Idan za a iya tunawa a ranar Laraba kotun ta dage zamanta zuwa ranar Alhamis domin bangaren da ake kara ya gabatar da hujjar da za ta sa a yi watsi da shari’ar, masu kara kuma su yi martani.