✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar N287m: EFCC ta tsare tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai, Patricia Etteh

Shekara 15 bayan badakalar kwangilar da ta sa ta sauka da kujerar Shugaban Majalisar Wakilai.

Hukumar YaKi da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan Najeriya, Patricia Etteh, kan karkatar da Naira miliyan 287.

Shekara 15 ke nan bayan wata dambarwar almundahana ta sa Majalisar Wakilai ta yi yunkurin tsige Misis Etteh daga shugabancin majalisar a shekarar 2007.

A wannan karon, EFCC ta tisa keyar Patricia Etteh ne kan zargin almundahanar da Naira miliyan 287 na kwangila a Ma’aikatar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).

EFCC na zargin Patricia Etteh ta karbi Naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited, wanda NDDC ta bai wa kwangilar Naira miliyan 240 a shekarar 2011.

A halin da ake ciki EFCC ta bukaci tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ta yi bayani kan shigar kudin asusunta amma ta gaza ba da cikakkiyar hujja.

EFCC ta nemi jin me ya kai kudaden asusun ajiyarta na banki, tunda ba ita ce darakta ba.

An zabi Patricia Etteh a matsayin Shugabar Majalisar Wakilai a 2007, sai dai ta yi murabus bayan watanni bisa zargin facaka da wasu kudade.

A lokacin, ’yan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga shugabancin su, matakin da kafin daga bisani ta yanke shawarar sauka daga mukamin.

A wancan lokacin ana zargin ta da ware wasu makudan kudade don ba da kwangilar gyaran gidan da aka tanadar wa Shugaban Majalisar.

Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar Majalisar Wakilai a tarihi.

Wannan samame na zuwa ne kwana biyu bayan da EFCC ta cafke Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, bisa zargin karkatar Naira biliyan 80.

Cin hanci da rashawa na daga cikin manyan matsalolin da suka yi wa Najeriya katutu, kuma babban abin da ke kawo wa kasar koma baya musamman a bangaren tattalin arziki.