✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar N80bn: Ministar Kudi ta dakatar Akanta-Janar, Ahmed Idris

Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan EFCC ta kama shi

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta dakatar da Akanta-Janar na Najeriya, Ahmed Idris daga mukaminsa saboda zargin badakalar Naira biliyan 80.

Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta cafke shi saboda zargin karkatar da kudaden.

Zainab ta sanar da korar ce a cikin wata wasika da ta aike wa tsohon Akanta-Janar din dauke da sa-hannunta, mai kwanan watan 18 ga watan Mayun 2022.

Wasikar ta ce, Biyo bayan korarka da EFCC ta yi, saboda zargin karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 80, ina sanar da kai cewa an dakatar da kai daga mukaminka daga ranar 18 ga watan Mayun 2022, ba tare da biyanka kowanne kudi ba.

“An dauki matakin ne don a samu damar aiwatar da cikakken bincike a kanka ba tare da katsa-landan ba, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati suka tanadar.

“A iya tsawon wannan lokacin, ana so ka kauracewa ofishinka kuma kada ka halarci kowane irin taro ko ofishin gwamnati, har sai an gayyace ka,” inji wasikar.