✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bakano ya rasu a garin ciro waya daga sokawe

Ya rasu a ramin bahaya, wato sokawe a unguwar Jigirya, Karamar Hukumar Nassarawa

Wani mutum mai shekara 40 ya rasu a ramin bahaya, wato sokawe a unguwar Jigirya da ke Karamar Hukunar Nasarawa ta Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis kamar yadda sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana.

“Wani kiran gaggawa ya shigo mana da karfe 1:30 na rana daga wani mai suna Abbas Abubakar cewa wani mutum ya fada sokawe.

“Wayarsa ce ta fada masai shi ne shi kuma ya fito ya zo ramin domin dauko abarsa, sai aka samu akasi ya fada ciki, ya rasa ransa,” in ji kakakin.

A wani labarin kuma, kakakin ya ce sun ceto wasu yara biyu Fatima Lawan mai shekara 2, da Khadija Lawan mai shekara 9 sun da suka fada rijiya a kauyen Dan Gawo da ke Karamar Hukumar Bichi.

Jami’in hulda da jama’ar rundunar ya ce kiran gaggawa da wani dan Hisbah ya yi musu a ranar 27 ga watan Afrilu da karfe 5:35.

Ya ce lamarin ya faru ne bayan Fatima ta je diban ruwa a rijiya da kanwarta Khadija a goye a bayanta, sai santsi ya kwashe ta, ta fada tare da Khadijan a bayanta.