✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakin haure 21 sun mutu a ruwa

Wannan hadarin jirgi shi ne irinsa na biyu cikin kwana biyu da ya auku a yankin. 

Wasu bakin haure 21 ne suka hallaka bayan kwalekwalen da ke dauke da su ya nitse a gabar tekun Tunisiya.

Wani jami’in tsaro a yankin ya ce, wannan hadarin jirgi shi ne irinsa na biyu cikin kwana biyu a yankin da ya auku.

Kanar Houssem Ibebli daga hukumar tsaron kasar, ya ce masu gadin gabar tekun sun gano gawarwakin a tashar jirgin ruwa ta Sfad.

Rahotanni a ranar Asabar sun ce, akalla bakin haure 43 ne suka nutse a cikin jirgin yayin da aka ceto wadansu 84 bayan da wani jirgin ruwa ya kife da su a kusa da gabar tekun Tunisiya na Zarzis.

Mahukunta sun ce bakin hauren na kokarin tsallaka Bahar Rum daga Libya zuwa Italiya.

Kamar yadda bayanai suka ce, masu gadin gabar teku sun yi nasarar dakile ayyukan bakin haure 10 a cikin ’yan kwanakin nan tare da ceto mutum 158.