✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Balaguron Gwamna da Mataimakinsa ranar Hawan Nassarawa ya jawo cece-kuce a Kano

Gwamnati ta ce babu wata matsala tsakaninta da masarauta

Gwamnatin Jihar Kano ta yi karin haske kan rashin gudanar da Hawan Nassarawa a Sallar Bana kamar yadda aka saba yi a kowacce shekara.

Hawan wanda tsohuwar al’ada ce ta kusan shekaru 100 ana gudanar da shi a kowacce ranar biyu ga Sallah, in da Sarkin Kano ke kai ziyara gidan gwamnati, daga nan ya wuce zuwa gidansa da ke kan titin State Road.

To sai dai a bana an samu akasi inda Sarkin gidansa na Nasarawan ya zarce kai tsaye ba tare da kai waccan ziyara ba, wanda hakan ya janyo cece-kuce musamman a kafofin sada zumunta, saboda abu ne da ba a saba da gani ba.

Wannan ya sanya al’umma tofa albarkacin bakinsu da hasashe iri-iri kan dalilan da suke ganin su suka  janyo hakan, inda wasu ke cewa Sarkin ba shi da labarin Gwamnan da Mataimakinsa ba sa gari, har sai da ya je gidan Gwamnatin, labarin da gwamnatin ta musanta.

Babban mai ba wa Gwamnan Kano Shawara Kan Harkokin Masarautu, Tijjani Mailafiya Sanka, ya ce Sarkin na da masaniyar Gwamnan ba ya nan, kuma kasancewar hakan ba zai hana gudanar da hawan ba, ya sanya ya umarci Sarkin ya yi hawan  ba tare da kai wa gidan gwamnati ziyara ba.

Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu kiran gaggawa ne zuwa Abuja ranar Lahadi, kuma zai kwashe kwana hudu a can, yayin da Mataimakinsa ke kasa mai tsarki domin sauke farali.

“Kasancewar bisa al’ada Gwamna ko Mataimakinsa ne ke da alhakin karbar Sarki kuma ba sa gari, shi ya sanya Gwamna ya sanar da shi halin da ake ciki, inda ya umarce shi da ya gudanar da hawan ba tare da halartar gidan gwamnatin ba,” inji Mailafiya Sanka.

Kazalika ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka samu hakan ba a tarihin jihar, domin ko a baya da ake nada Sarakuna Amirul Hajji su tafi Saudiya, ba a ma hawan baki daya.

“Da haka nake sanar da al’umma cewa alakar gwamnatin Kano da Masarauta mai karfi ce, domin hatta ranar Sallah ma Gwamna da Sarkin tare suka yi Sallar Idi, kuma Gwamnan ne ma ya ja tawagarsa zuwa gidan Sarkin a Hawan Daushe,” inji shi.