Daily Trust Aminiya - Balahirar Fyade: Jan hankali ga iyaye da al’umma (3)

Hoto: Healthyplace

Balahirar Fyade: Jan hankali ga iyaye da al’umma (3)

Wannan ne ci gaban mukalar daga Babban Lauya, Ustaz Yusf O. Ali (SAN), fassarar Barista M. B. Mahmoud Gama:

A wani bincike da suka aiwatar, mai taken: “Violence Against Women: A Priority Health Issue,” Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ba da da kididdiga cewa, kusan yara mata miliyan 200 suka tsinci kansu a wannan matsalar ta fyade a 2012.

Kuma abin takaici, mafi yawan wadanda suka yi wa yaran fyade, inji rahoton, maza ne kuma sanannu ne, ba bare ba, ga su yaran.

Duk da an hakikance a kan cewa yin fyade ga kananan yara ya zama ruwan dare da ya game duniya amma har yanzu babu kididdiga isassu da suka ba da cikakken bayanin yawaitar fyaden a duniya, balantana ma nan Najeriya.

A Najeriya, rashin samun cikaken bayanin fyade ga yara da za a iya dogara da shi wajen hukunta masu laifin, na da alaka da wasu dalilai daban-daban da suka shafi samun cikaken bayani a kan yarinyar da aka yi wa fyaden.

Wadannan bayanai sun hada da: rashin samun cikakken bayani a kan shekarun yarinyar a lokacin da aka yi mata fyaden, rashin samun hakikanin alakar wacce aka yi wa fyaden da wanda ya yi da kuma kin bayyana wanda ya yi wa yarinyar fyaden, watakila saboda alakar ’yan uwantaka da ke tsakaninsu don gudun tonon sililin da ka iya biyo baya a cikin ’yan uwa.

A wani lokacin kuma ana kasa samun cikaken bayanin yin fyaden ne saboda gudun irin tsangwamar da ita yarinyar ka iya samu a cikin al’umma, wanda a wani lokacin, a wasu wuraren, kan iya shafar yiwuwar auruwar yarinyar bayan ta girma.

Wani lokacin kuma, shi wanda ya yi fyaden ne yake hada baki da likitan da ya duba yarinyar, ko ’yan sandan da suka binciki lamarin, don su ba da bayanin karya, sabanin hakikanin abin da ya faru.

Babu shakka, a ’yan kwanakin nan, fyade ga yara ya zama tamkar wata musiba ce da ta samu gindin zama a tsakanin mutanenmu.

Kwanan nan wasu ’yan uwa su biyu, ’ya’yan wani Fasto a Jihar Ebonyi suka yi fyade ga wasu yara ’yan uwan juna, daya ’yar shekara 7, dayar kuna ’yar shekara 9.

An ce sun yaudari yaran ne a cocin da babansu ke jagoranta.

Haka ma wata jaririya ’yar wata 8, aka samu mahaifinta ya yi mata fyade!

Har ila yau, a kwanakin baya aka samu yi wa kananan yara fyade a Funtuwa, Jihar Katsina na adadin yara da bai gaza 13 ba, wadanda aka yi wa yaran magani a Babban Asibiti na Funtuwa.

Kan haka, Babban Daraktan Asibitin, Dokta Tijani Bakori ya ce mafi yawan yaran da aka yi wa fyaden ya kai ga yi musu aiki a farjinsu, domin a cewarsa, duk yaran da aka yi wa fyaden ’yan kasa da shekara 13 ne kuma dukkansu sun fito ne daga gidajen marasa karfi.

Yin fyade ga yara maza

Haka labarin yake ta fuskar yin fyade (luwadi) ga kananan yara maza, kamar yadda bincike mai taken: “Child Victim of Sedual Abuse in Nigeria” ya nuna.

Kodayake a wani binciken da Abdulkadir I. ya yi mai taken: “Child Sedual Abuse in Minna Niger State” ya nuna, babu wani bayani da ke tabbatar da yawaitar yin fyade (luwadi) ga kananan yara maza, wanda hakan a cewarsa, ba ya rasa nasaba da, ba kamar mata ba, kin bayyana fyaden da ake yi musu.

Saboda haka, a cewar binciken, wannan kuma ba ya nuna ba a yi wa yara maza fyaden.

Ita ma Hukumar ’Yan Sanda ta Jihar Ogun, ta taba kama wani malamin makaranta da ke koyarwa a wata makaranta da yi wa wani dalibinsa fyade.

Mahaifin yaron ne ya kama shi dumu-dumu yana luwadi da yaron nasa, a yayin da ya zo daukarsa zuwa gida.

Yaron ya ce ba wannan ba ne karo na farko, ya sha yi masa amma yana tsorata shi a kan kada ya fada wa kowa.

Kodayake, yin fyade ga kananan yara maza ya karanta, to amma dai duk da haka, yana fama da rashin kulawa da ta kamata kamar yadda aka ba na mata muhimmanci.

Hakkin Iyaye da Al’umma Wajen Kula da Yara:

Da yake daidai gwargwado, mun tabo dokokin da suka ba wa yara kariya don kange martabarsu da mutuncinsu da al’umma ke yi wa hawan Kawara, a karkashin wannan maudu’i kuma dai, za mu shafi kan dokokin da suka wajabta wa iyaye lura da ’ya’yansu ta fuskoki iri daban-daban.

Alabashi daga bisani kuma sai mu karkare da irin gudunmuwar da al’umma ya kamata ta bayar don cin kwalar wannan babban laifi da ya zama ruwan dare gama duniya a cikin al’ummarmu.

Babu ko shakka, iyaye na da babban tasiri ga rayuwar ’ya’yansu tun daga lokacin da Allah Ya ba su kyautarsu har zuwa lokacin girmansu.

Saboda haka, iyaye a wajen ’ya’yansu tamkar wata fitila ce mai haska musu gaba cikin rayuwarsu dukkanninta.

Fahimtar haka ce ta sa a karkashin Sashi na 14 na Kundin Hakkin Yara aka samar da cewa, kowane yaro/yarinya na da hakkin samun kulawar iyaye, da ba su kariya daga kowace irin cutarwa, da kuma daukar nauyin rayuwarsu.

A Sashi na 14 Karamin Sashi na (2) na dokar ya ci gaba da cewa:

“Kowane yaro yana da hakkin samun kulawa daga iyayensa, ko wadanda Allah Ya dora wa hakkin kulawa da shi, gwargwadon ikonsu.

“Sannan a duk lokacin da ya dace, yana da ikon ya nemi wannan hakki nasa a kotu”.

Shi kuwa Sashi na 2 na Kudin, fadadawa ya yi, inda ya ce dole ne ya samu waccar kulawar daga iyaye, ko masu kula da shi ko al’umma da hukumomi da kungoyoyi da hukumomin da aka yi su musamman don kula da yara. Duk fa don samun kyautatuwar rayuwar su yaran.

Sannan duk wadannan hukumomi da kungiyoyi da dokar ta zayyana su a sama, to tilas ce su ba da kulawar ta fuskar ba su natsuwa da ingantacciyar lafiya da walwala, gwargwadon yadda dokokin da suka kafa hukumomin da kungiyoyin suka tanada.

Daga nan sai Sashi na 11 na Kundin ya dora da cewa:

“Kowane yaro yana da hakkin a kare masa mutuncinsa a matsayinsa na mutum kuma kare mutuncin nasa na nufin, dole ne, kada a cutar da shi ta fuskar: (a)-jikinsa ko hankalinsa, ko wulakanta shi ko aikata masa babban laifi kamar yi masa fyade, ko (b)-azabtar da shi ta fuskar aikata masa rashin imani (wai don hukunta shi, ko (c)-ci masa mutunci ba-gaira-ba-dalili, ko (d)-iyaye ko wadanda suke kula da shi da kungiyoyi ko Hukumar Makaranta ko wani da yake da iko da shi yaron, tursasa shi yin wani aiki mai kama da na bauta”.

Daga nan sai kundin, tun daga Sashe na 15 Karamin Sashe (1) zuwa Karamin Sashe na (7) ya yi tilawar hakkin da yara ke da shi wajen iyaye da hukumomi don ba su ilimi tun daga matakin firamare har zuwa Babbar Sakandare. Kuma dokar ta tanadi hukunci ga duk mahaifin da ya gaza sauke wannan hakki da gangan.

Duba ga dokokin kawai, zai tabbatar wa da mai karatu cewa, lallai iyaye da wadanda Allah Ya dora wa hakkin kula da yaran da kuma al’umma baki daya, akwai hakkoki da dama da suka ratayu a wuyansu, tun daga ciyarwa, tufatarwa, samar da muhalli da ba da kulawa, da ilimanatarwa da tarbiyantarwa, da sauransu, da dokokin suka nemi da su sauke su.

Idan kuwa hakan ba su samu ba, sai dokokin suka yi tanadin hukuce-hukunce masu tsauri da za su fada a kan duk mahaifin da bai cika su ba.

Karin Labarai