✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ballon d’Or: Messi ya lashe Gwarzon Dan Kwallon Duniya karo na 7

Cristiano Ronaldo ne a matsayi na shida a jerin wadanda suka yi zarra a Ballon d'Or a bana

Dan wasan kungiyar PSG da kasar Ajantina, Lionel Messi, ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya na 2021.

Karo na bakwai ke nan da Messi, mai shekara 34 ya lashe kambun, a yayin da Cristiano Ronaldo ke biye masa da guda biyar.

Kafin wannan karon, Messi ya lashe kambun na Ballon d’Or a shekarun 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da 2015 da 2019 sai kuma na bana.

Robert Lewandowski na kasar Poland da kungiyar Bayern Munich shi ne Dan Wasan Kwallon Kafa na Biyu a Duniya.

Shi ne kuma ya kuma kambun Dan Wasan Gaba na Duniya, inda ya yi wa Gerd Muller zarra wurin yawan zura kwallaye a kaka daya ta Gasar Bundesliga ta kasar Jamus.

Jorginho na kungiyar Chelsea da kasar Italiya shi ne ya zama na uku a jerin ’yan kwallon duniya na bana.

Karim Benzema na kungiyar Real Madrid da kasar Faransa, shi ne na hudu, a matsayi na biyar kuma N’Golo Kante na kungiyar Chelsea.
A bana Cristiano Ronaldo na kasar Portugal da kungiyar Manchester United, shi ne ya zo a matsayi na shida a jerin ’yan wasan da suka yi zarra.
Mohammed Salah shi ne wanda ya zo na bakwai, a yayin da kungiyar Chealsea ta lashe kyautar Gwarzuwar Kungiyar Kwallon Kafa ta 2021.
Kungiyar ta Chealsea wadda Thomas Tuchel yake jagoranta, ita ce ta lashe Gasar Zakarun Turai, sannan ita take saman teburin Gasar Firimiyar Ingila.