✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ballon d’Or: Mutum hudu da ka iya lashe Gwarzon Dan Kwallon Duniya na bana a yau

A yau Litinin, 29 ga Nuwamba ne za a bayar da Gwarzon Kwallon Kafa na duniya wato Ballon d’Or na bana a birnin Paris na…

A yau Litinin, 29 ga Nuwamba ne za a bayar da Gwarzon Kwallon Kafa na duniya wato Ballon d’Or na bana a birnin Paris na Faransa.

Idan ba a manta ba, a kakar bara ba a sanar da wanda ya lashe gasar ba saboda annobar Covid-19 da ta jawo cikas a kusan komai na duniya.

A bana, an sanar da mutum 30 da dayansu zai lashe kambun, ciki har da mai rike da kyautar, Lionel Messi na kungiyar PSG ta Faransa.

Aminiya ta kalato mutum hudu da take ganin a cikinsu ne daya zai lashe kambun.

Lionel Messi: PSG

A kakar bana, Messi ya zura kwallo 41, ya taimaka an ci kwallo 17. Ya lashe kofin Copa America da Copa del Rey.

A yanzu haka shi ne ke rike da kambun, kuma ya lashe kyautar sau shida, daya sama da Ronaldo mai guda biyar.

Messi ya fara ne daga Barcelona, sannan ya koma PSG  a yanzu.

Magoya bayansa suna ta kamfe a kafafen sadarwa cewa ‘a gida za a barta’ wato a Paris za a yi taron, kuma a Paris wato kulob din da Messi (PSG) za a bar kambun.

Messi rike da kofin Copa America da ya jagoranci Ajantina ta lashe
Hoto: Marca.com

Robert Lewandowski : Bayern Munich

A kakar bana, Lewandoski ya ci kwallo 64, ya taimaka a zura kwallo 10, sannan ya lashe kofin Bundesliga da Club World Cup da DFL-Supercup

A kakar bara ce aka fi yin tsammanin Lewandowski zai lashe kambun, sai annobar covid-19 ta masa cikas.

Sai dai bayan da aka dawo tamaula bayan dogon hutun, Lewandowski ya daura ne daga inda ya tsaya, musamman wajen zura kwallaye a raga. Sai dai kasarta ta Polanda ba ta tabukawa sosai.

Magoya bayansa suna cewa ganin yadda aka ‘hana’ shi lashe kambun a kakar bara, sannan ya kokarta wajen daurawa a bana, ko da akwai wadanda ke gaban shi, shi ya kamata a ba kambun a birnin Paris.

Robert Lewandoski
Hoto: Goal.com

Jorginho: Chelsea

Jorginho dan wasan Chelsea da Italiya ne. A kakar bana ya zura kwallo 9, ya taimaka an ci uku. Ya lashe Kofin Duniya da Zakarun Turai da UEFA Super Cup.

A kofuna manya da ya lashe a kulub da kasa, duk yana cikin zaratan ’yan wasan da suka taimaka wajen samun nasaririn.

Shi ne ya lashe kambun Gwarzon Dan Kwallon Turai, wato UEFA Player of the Year, wanda hakan ya sa wasu suke ganin kamar sharar faga ce domin lashe babban kambun a yau.

Duba da manyan kofuna biyu na duniya da lashe, da taimakon da ya yi wa kulob dinsa da kasar wajen lashe kofuna ababen dubawa ne matuka.

Jorginho rike da Kofin Duniya da ya lashe da Italiya
Hoto: en.as.com

Cristiano Ronaldo: Manchester United

A kakar bana, Ronaldo ya zura kwallo 43, ya taimaka an zura kwallo 6. Ya lashe Coppa Italia da Supercoppa Italiana.

Ronaldo ya fara ne daga kungiyar Juventus ta Italiya, sannan ya koma Manchester United a yanzu.

Shi ne ya fi zura kwallo a gasar Seria A ta bara, sannan ya fi zura kwallo a gasar Europe 2020, sannan ya kafa tarihin zama wanda ya fi zura kwallaye a cikin maza ’yan kwallo.

Sannan komawarsa Manchester United da yadda ya nuna bajinta abin lura ne musamman ganin yanayin shekarunsa.

Ronaldo rike da kofin Super Cup na Italiya Hoto: sportkeeda.com